1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages


 

Duniyar ɗan Adam | 01.03.2010

Fasahar ƙera kaya daga shara

 

Hali na ƙuncin na tilasta mutane ƙirƙiro sabbin hanyoyin cin abinci

 

Alƙalumma sun yi nuni da cewa kowane Bajamushe na samar da shara rabin tan a kowace shekara, wato kimanin shara tan dubu 37 kenan aka kwashe zuwa wuraren ƙona su ko sarrafa su zuwa takarda kamar yadda aka sani a nan. To sai dai a ƙasashe masu tasowa na Afirka ko Asiya ko Latunamirka, talakawa ne ke sarrafa sharar da suka tsinta a juji, suna ƙera kayaki da su. Yanzu haka dai irin waɗannan kayan na samun karɓuwa a nan Turai a matsayin kaya mai kyan fasali.

Martina Zenker mai shagon Mamaafirka a birnin Düsseldorf na nan Jamus ta yi bayanin irin kayakin da ta ke sayarwa a shagon na ta.

"A nan ana iya ganin wani mutum mutumin mala´ika daga Madagaska wanda aka sarrafa da gwangwanin maganin feshin ƙwari."

Martina Zenker dai na da kwando guda cike da waɗannan kayan da aka sarrafa da gwangwanin maganin kashe ƙwari ko jakkunan laida da abin hannu da aka yi da wayoyin tarfo. Kayan da ke cikin shagon Mamaafirka dai sun samo asali ne daga juji ko sharar da aka zubarwa a gefen hanya a birane kamar Capetown da Johannesburg a Afirka Ta kudu ko Dakar a Senegal. Tuni fasahar ƙera kayaki daga shara a Afirka ta samu karɓuwa a ƙasashen Turai inda yanzu haka baje su a gidaje ya zama sabon yayi, inji Zenker sannan sai ta ƙara da cewa.

"Sharar ta yi mana yawa ba mu ma san yadda za mu yi da ita ba. Muna maraba da wannan fasahar daga Afirka da ma wasu ƙasashe inda bisa dalilai na halin ƙunci mutane ke samar da kayaki masu amfani daga sharar da muke zubarwa a juji."

Fasahar sarrafa kayan daga ƙasashe masu tasowa ya dace da tsarin kare muhalli na ƙasashe masu ci-gaban masana´antu. Saboda haka Martina Zenker wadda a halin yanzu ta buɗe hanyar saye da sayarwa ta intanet kuma tana sayarwa kantuna kimanin 140 kayaki daga Afirka, ta fara tunanin shiga wannan harka ne a shekarar 1994 sanda ita da mijinta suka yi rangadin wasu ƙasashen Afirka tsawon shekaru biyu. Tun a wancan lokaci ta ga yadda yara da kansu ke ƙera kayakin wasansu daga shara. Kuma yanzu ake sayarwa a wasu kantuna.

Lukas Plum shi ma mai kantin sayar da kayakin wasan yara ne da sauran kayakin da aka sarrafasu daga shara kamar gwangwanin timatir ko kayan ado da ake yi da tsaffin kwalaye daga ƙasashe masu tasowa. To sai dai saɓanin Mamaafirka, Lukas Plum wanda shagonsa ke a birnin Kolon, yana sayar da dukkan kayaki masu amfani a rayuwar yau da kullum.

"Alal misali suna ƙera butan gadina da tsoffin gwangwani. Ba kai tsaye suke tunanin ƙera kayakin ba, a´a suna amfani da wasu hanyoyin ƙere-ƙere da suka saba tun a lokutan baya."

Tun kimanin shekaru huɗu da suka gabata wata gidauniya dake garin Herford na wannan jiha ta North Rhein Westfaliya ke ba da lambar yabo ga masu sarrafa shara don ƙera kayaki masu amfani musamman daga ƙasashe masu tasowa.

Mawallafa: Sarah Hofmann/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmed Tijani Lawal

 
 

Send us an e-mail »Send »Print »

More on the topic

 
Share this article


 
Bikin kiɗa na Beethoven a Bonn

Bundesliga 2010/2011
Bajamushe a Wurin Aikinsa

Shiri kan rayuwa a Jamus - Na harshen Hausa a cikin shirye-shiryenmu kowace Talata da Alhamis.

DW-TV EUROPE live

drive it!

We're sorry, due to legal issues this content can not be transmitted as live stream.

If you are inside the United States, it is still possible for you to enjoy DW-TV. For more information, please click here.