1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages


 

Zamantakewa | 23.10.2009

Shekaru 20 da rushewar katangar Berlin

 

Eric Singh ya shaidar da rushewar katangar Berlin

 

Neman tuna  yadda rayuwa ta kasance a yankin Jamus ta gabas, al'amari ne da kan kasance mai matukar sarkakiya ga su kansu  mazauna wannan yanki. Suma baki yan ci rani da suka taba zama a yankin na Jamus ta gabas, basa samun saukin bayanin irin  halin da suka zauna karkashin sa a yankin. Daya daga cikin irin wadannan baki da suka  zauna a  Jamus ta gabas din har zuwa ranar  tara ga watan Nuwamna na shekara ta 1989, shine  Eric Singh. Haifaffen Afrika ta kudu, Singh ya tsere ne zuwa Jamus ta gabas daga Durban, domin ya kauracewa gallazawa a kasar sa.

Daga   Berlin ta gabas, dan gwagwarmayar na kungiyar ANC  yaci gaba da nuna adawar sa ga  mulkin wariya, inda har ma ya rika samun goyon baya da taimakon kudi daga hukumomin wannan yanki. Har ma bayan rushewar katangar ta Berlin,  Eric Singh yaci gaba da zama a  Berlin, inda a yanzu  yake tuna rayuwa a Jamus ta gabas  da rushewar katangar Berlin.

Shin ana iya cewar  wannan  hira da manema labarai ya  canza al'amuran duniya.  Wannan dai tabbas haka yake,  a bisa ra'ayin yan jarida da suka hallara, suka saurari jawabin  Günter Schabowski,  kakakin gwmanatin kwaminisanci ta Jamus ta gabas, ranar tara ga watan Nuwamba na shekara ta 1989 a Berlin  ta gabas. A wannan rana, Schabowski ya sanar da   matakan sassauta tafiye-tafiye zuwa ketare ga  yan Jamus ta gabas. Eric Singh ya halarci  wannan taro na manema labarai, saboda daga   can Berlin ta gabas ya rika  aikawa mujallu dabam dabam   sharhuna da rahotanni. Saboda haka ma  Singh yace yayi imanin  ya  kasance cikin wadanda suka shaidar da wani al'amari na tarihi. Yace:

"Na bi wannan taro na  yan jarida a tsanaki, kuma naji tambayar da Ricardo Ehrmann daga Italiya yayi, inda ya tambayi shin wane lokaci ne za'a bude iyakokin  na Jamus ta gabas? Shi kuma Schabowski ya amsa da cewa yau".

Jim kadan kuwa bayan  wannan hira da yan jaridu,  wanda ma gidan television na hukuma ya nuna kai tsaye,  aka fara samun yan Jamus ta gabas da suka yi kasadar zuwa kan iyakokin da suka raba tsakanin Berlin ta gabas da Berlin ta yamma. Masu tsaron kan iyakokin, wadanda ma  tururuwar jama'a  ta nemi fin karfin su, suka  kyale  jama'a su tsallaka  zuwa daya bangaren, wanda  har ya zuwa wannan lokaci aka haramtawa  yan Jamus ta gabas shi. Nan da nan kuwa   labarin haka ya watsu ko ina, inda  jama'a  suka rika cunkoso a wuraren kan iyaka a Berlin ta gabas, domin neman tsallkawa zuwa yamma da kuma samun yancin su. Ya zuwa tsadar dare  aka bude dukkanin iyakokin, katangar Berlin ta zama sai labari. Shi kansa Eric Singh ya shaidar da  wannan babban abu na tarihi ne a washegari, inda ya shiga  jirgin kasa daga tashar Friedrichstrasse a Berlin ta gabas zuwa yankin  Berlin ta yamma. Yace:

"Daga Friedrichstrasse na isa kan iyaka, inda na taras da dubban jama'a, musmaman matasa.  Daga nan  muka tsallaka kogin Spree zuwa Berlin ta yamma.  Na kuma fahimci yadda dimbin jama'a sukai ta nuna bukatar su ta zuwa ga samun yanci, saboda ni kaina na kasa samun damar  tserewa daga Afrika ta kudu lokacin da naso, saboda a matsayi na na  dan gwagwarmaya adawa da wariya, bani da yancin fita zuwa ketare, saboda bani da paspo".

A yau, Eric Singh  yana nuna matukar godiyar sa ga dukkanin taimako da goyon bayan da ya samu daga Jamus ta gabas kasar da a bana, shekaru ashirin kenan da  bacewar ta. Yace duk da  mummunan kasawar yankin  a bangaren democradiya da kuma  matakai masu tsanani kan  yan adawa, amma  Jamus ta gabas ta bada gudumuwa mai yawa a gwagwarmaya kan gwamnatin wariya ta Afrika ta kudu. Yace:

"A nan  ko da shike mutane basu da yancin tafiye-tafiye  yadda suka so, amma  sun karbi wannan hali   cikin kwanciyar hankali. Na kan tattauna haka din da matata ta, wdada ita  ma yar Jamus ta gabas ce. Takan ce a da can nayi    rayuwa ce ba tare da hatsaniya ba, amma ba haka   abin yake ba a yanzu. Bayan da  aka  rushewa kasar,  ta rasa aikin ta a matsayin mai fassara saboda wai ta tsufa. Ba kuwa ita kadai ba, jama'a da dama sun shiga irin wannan hali.

 Yanzu Eric Singh yana zaune cikin farin ciki da   jin dadi da matar sa a Berlin. Dan jaridar da yayi ritaya har yanzu  yana  da  alaka ta kurkusa tare da  Afrika ta kudu, kasar da tun bayan   kawo karshen mulkin wariya yake mallakar paspo din ta.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Tijani Lawal

 

Umaru Aliyu

 

Send us an e-mail »Send »Print »

More on the topic

 
Share this article


 
Bajamushe a Wurin Aikinsa

Shiri kan rayuwa a Jamus - Na harshen Hausa a cikin shirye-shiryenmu kowace Talata da Alhamis.

DW-TV EUROPE live

motor mobil

We're sorry, due to legal issues this content can not be transmitted as live stream.

If you are inside the United States, it is still possible for you to enjoy DW-TV. For more information, please click here.